Connect with us

Labarai

Gobara ta yi sanadiyar rasuwar iyalai a jihar Kaduna

Published

on

Gobara ta yi sanadiyar mutuwar wata mata mai shayarwa tare da jaririnta da kuma wasu kananan yara guda uku a jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a Layin ‘Yan Tanki da ke Unguwar Rigasa a yankin karamar hukumar Igabi a jihar ta Kaduna.

Shaidun gani da ido sun ce makwabta sun fasa bandakin gidan domin ceto mutanen, sai dai mijin matar kawai mai suna Sani Yahaya Jumare  su ka samu a raye wanda daganan su ka garzaya da shi, Asibiti.

Bayanai sun tabbatar da cewa gobarar wadda aka alakantata da tartsatsin wutar lantarki, ta tashi ne da misalin karfe biyu na dare lokacin da mutanen ke tsaka da bacci.

Asibitin kashi na Dala ya fadakar da dalibai illar gobara

Dole ne Al’umma su hada kai da hukumar Kashe gobara-Usman Alhaji

Samar da lantarki mai amfani da hasken rana ne kadai zai magance tashin gobara a kasuwanni

Wadanda suka rasa rayuka sun hada da Rukayya wadda ita  mai dakin sa da jaririnta mai suna Rilwan da wasu ‘ya’yanta da suka hada da: Rabi’atu ‘yar shekarar biyu da Khadija mai shekaru shida da kuma Hajara ‘yar shekaru bakwai wadda ita ‘Ya’ ce ga kanwar mai gidan.

Sai dai daga nan Kano mun tuntumbi kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP Yakubu Sabo wayar sa a kashe amma kuma za mu cigaba da tuntubar sa don jin karin bayani

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,784 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!