Labarai
Matatar Dangote na shirin fara rarraba Fetur a fadin Najeriya

Matatar mai ta Dangote ta sanar da cewa za ta fara rarraba mai daga matatar zuwa gidajen mai da ke faɗin kasar nan.
Dangoten ya yi alƙawarin sayo manyan motocin dakon mai masu amfani da iskar Gasa na CNG, kusan 10,000, da kawo yanzu haka ya sayo 4,000 daga ciki, inda ya yi alƙawarin ɗaukar man daga matatarsa zuwa gidajen man da suka sari man nasa a kyauta.
Sabon matakin na Matatar Man ta Dangote, ya jawo suka da cece kuce daga ƙungiyar masu dakon man fetur da rarraba shi zuwa gidajen man ƙasar, ta NUPENG da suka zargi Dangote da yi musu kafar Ungulu.
You must be logged in to post a comment Login