Labarai
Matatar Dangote ta musanta cewa NNPCL ya ƙara mata adadin yawan ɗanyen mai zuwa ganga Miliyan 7

Matatar mai ta Dangote ta musanta rahotannin da ke cewa kamfanin mai na kasa NNPCL ya ƙara mata adadin yawan ɗanyen mai zuwa ganga Miliyan bakwai a watan Mayu.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Jami’an matatar ta ce ba su da tabbacin wannan rahoto, inda ta bayyana cewa abin da ake sa ran samu shi ne kusan ganga miliyan 6.15a.
Sanarwar ta ce matatar na buƙatar sama da ganga Miliyan 19 kowanne wata, amma tana samun kusan Miliyan biyar ne kawai, lamarin da ke kawo cikas ga aikin matatar
A nata ɓangaren, NNPCL ta ce tana ƙoƙarin ƙara samar da ɗanyen mai domin tallafa wa tace mai a cikin gida.
Masana tattalin arziki sun shawarci gwamnati ta kayyade farashin ɗanyen mai ga matatar, domin rage tashin farashin fetur da kuma dakile hauhawar sa a cikin gida.
You must be logged in to post a comment Login