Kasuwanci
Matatar Mai ta Dangote ta sake rage farashin Fetur

Matatar Man Fetur ta Dangote, ta sake rage farashin kowace Litar mai da kimanin Naira 10, daga Naira 835 zuwa 825 kan kowace lita.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wasu majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin sun bayyana cewa, tun da farko, ‘yan kasuwar sun biya Matatar Naira 835 kan kowacce lita afin daga baya, aka mayar musu da ragin Naira 10 bayan sun yi dakon man daga matatar.
Wata majiya ta tabbatar da cewa Matatar man ta Dangote ta fara bayar da rangwame kan kayayyakin da take samarwa, ba tare da sanarwa a hukumance ba amma an tura wa ‘yan kasuwar da rangwamen a asusun su bayan sun fitar da man daga Matatar.
Haka kuma, ana kyautata zaton cewa, ragin na da nasaba da sabunta tsarin sayen danyen mai da takardar Naira, biyo bayan dakatarwar da aka yi na wucin gadi.
You must be logged in to post a comment Login