Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Matsalar tsaro: Masu garkuwa da mutane sun sace wasu tare da ƙona motar jami’an tsaro a Kano

Published

on

Wasu ƴan bindiga sun yi awon gaba da mutane biyu tare da hallaka wani guda a garin Falgore na ƙaramar hukumar Rogo.

Lamarin ya faru ne a daren jiya inda suka afka wa gidan wani attajiri a garin Alhaji Ishu Mai Taki Falgore.

Ƴan bindigar sun yi awon gaba da matarsa da kuma ɗansa guda ɗaya.

Attajirin Alhaji Ishu Mai Taki ya tabbatarwa da Freedom Radio faruwar lamarin sai dai ya ce, ba zai ce komai a kai ba a halin yanzu.

Haka kuma ƴan bindigar sun buɗe wuta kan motar jami’an sintiri da suka haɗa da ƴan sanda da bijilante wanda kuma suka hallaka wani jami’in bijilante guda ɗaya a cewar wani mazaunin garin.

Daga bisani kuma sun ƙone motar jami’an sintirin ƙurmus.

Shaidun gani da ido sun ce da safiyar Litinin ne jami’an tsaro suka je garin inda suka ɗauki gawar wanda ya rasu.

Mun tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa wanda ya tabbatar da faruwar lamarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!