Labarai
Matsalar Tsaro: Sarkin Kano Ya Kalubanci Minista Kan Amfani Da Fasaha zamani
Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya ce ya kamata Ministan Sadarwa, Bosun Tijani, ya tabbatar ana amfani da fasahar zamani da kuma kwarewarsa wajen yakar kalubalen tsaro a Najeriya.
Sarki Aminu Ado Bayero wanda ya karbi bakuncin ministan a fadarsa a safiyar Alhamis, ya bayyana cewa minisan na da babban rawan da zai taka a yaki da matsalar tsaro, musamman a wannan yanayi da ’yan bindiga suka hana al’umma sakat.
Inda Sarki ya ce “Mu kuma a bangarenmu za mu ci gaba da yi maka addu’a domin samun nasara a wannan aiki,”
Ministan dai ya kawo ziyara Kano ne domin halartar Babban Taron Majalisar Sadarwa, Kirkira da Tattalin Azikin Zamani ta Kasa (NCCIDE) karo na 11.
Da yake mayar da jawabi, ministan ya ba wa Sarkin Kano da al’ummar Najeriya, tare da bayar da tabbacin cewa zai yi iya kokarinsa wajen sauke duk nauyin da ya rataya a wuyansa.
“Da yardar Allah ba za mu yi kasa a gwiwa ba, wajen sauke wannan nauyi na al’umma da aka dora mana,” in ji ministan wanda ya samu rakiyarn manyan jami’an hukumomin da ke karkashin ma’aikatarsa.
You must be logged in to post a comment Login