Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarkin Kano ya yi kira ga al’umma su bai wa jami’an sunturi hadin kai

Published

on

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi kira ga  al’umma su  dinga baiwa  jami’an  sunturi gudunmawar da ta dace don dakile matsalar tsaro a kasar nan.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne ta bakin wakilin fuskar Arewa a karamar hukumar Dala, Alhaji Sayyadi Muhammad Yola wanda ya wakilce shi ya yin da kungiyar sa kai ta Vigilante ke bude sabon ofishinta a karamar hukumar Dala.

Ya ce, yana da kyau al’ummar gari su rika samar da kayayyakin da za a rika amfani da su don gudanar da aikin tsaro a yankunan su.

A nasa jawabin shugaban kungiyar ta ‘yan sunturi na Vigilante a nan Kano, Muhammad Kabiru Alhaji, ya ce, duba da shigowar damuna ya sanya kungiyar ke kara fadada ofisoshinta a fadin jihar Kano, kuma shi wannan ofishin da aka bude a Unguwar Yalwa zai zama babban ofishin kungiyar a karamar hukumar Dala.

Wakilin mu Abubakar Tijjani Rabi’u, ya rawaito shugaban taron Alhaji Yusuf Ibrahim Wakilin Dukiya, na cewa, ofishin zai  yi  aiki ne a cikin unguwanni sama da Talatin dake fadin karamar hukumar ta Dala.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!