Labarai
Mayakan Boko Haram sun kai hari a garin Chibok na jihar Borno

Wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai hari a ƙauyen Awapul da ke ƙaramar hukumar Chibok a jihar Borno.
Rahotanni sun ce maharan sun shiga yankin ne da misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare, inda suka rika harbe-harbe tare da ƙona gidaje da shaguna.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Nahum Daso, ya tabbatar da aukuwar harin, inda ya ce babu asarar rayuka, sai dai an lalata dukiyoyi.
Wasu mazauna yankin sun ce maharan sun shafe sama da awa guda suna barin wuta, lamarin da ya tilasta wa mutane da dama tserewa domin samun mafaka.
Wannan hari na zuwa ne ƙasa da awa 24 bayan wani makamancin hari da aka kai sansanin ‘yan gudun hijira a Damasak, inda aka kashe jami’an tsaro da kuma lalata dukiyoyi.
You must be logged in to post a comment Login