Labarai
Mazauna Durumin Iya sun yi taron shirin gudanar da aikin gayya

Mazauna unguwar Durumin Iya da ke yankin ƙaramar hukumar Birni ta Jihar Kano, sun gudanar da taro domin tsara yadda za su gudanar da aikin gayya domin magance barazanar ambaliyar ruwa a daminar bana.
Mai unguwar yankin na Durumin Iya, Malam Jamilu Umar, ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai.
Mai unguwar, ya ce, taron ya samu halartar matasa da dattijan unguwar, inda aka cimma matsaya kan tattara kuɗaɗe da haɗa hannu domin shawo kan ambaliyar da ke barazana yayin da Damina ke ƙara kankama.
Malam Jamilu Umar, ya nuna farin cikinsa kan yadda al’umma suka haɗu waje guda, tare da yin kira ga shugabanni su mara wa shirin nasu baya.
Za dai a gudanar da aikin gayyar ne a ranar Lahadi mai zuwa.
You must be logged in to post a comment Login