Labarai
Mazauna Kabo sun nemi daukin gwamnatin Kano bisa zargin kwace musu Gonaki

Mazauna garin Kanye Kwanar Kabo a Kano, sun zargi wasu mutane da kokarin karbe musu Gonakin da suka mallaka fiye da guda dari bakwai, in da suke zargin wasu mutane da ke cewa gwamnati ce ta aika su domin yin aiki kan gonakin.
Wasu daga cikinsu da suka gudanar da wani gangami a ranar Alhamis sun shaidawa Freedom Rediyo cewar ba su da tabbacin gwamnatin Kano ce ke son karbar wuraren nasu.
Masu korafin sun bukaci gwamnatin jihar da ta yi wa kowanne bangre adalci.
Sai dai ko da muka tuntubi ma’aikatar Kasa da tsare-tsare ta jihar Kano, ta ce, da sahalewar gwamnatin Kano ake gudanar da wannan aiki kuma ba za a wofantar da masu wuraren ba kamar yadda Surveyor General Usman Umar Bichi, ya bayyana.
You must be logged in to post a comment Login