Connect with us

Labarai

MDD ta kaddamar da neman taimako domin tallafawa Sudan

Published

on

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya tare da ƙungiyoyi abokan hulɗa 123 sun ƙaddamar da neman gudummawar sama da  dala biliyan 1, domin taimaka wa miliyoyin yan ƙasar Sudan da suka tsere daga ƙasar su da yaki ya dai dai ta.

 

Wannan na da nufin kai agajin gaggawa ga  ‘yan Sudan miliyan 5,  da ke gudun hijira a ƙasashe bakwai makwabta da suka hada da Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya da Chadi da Masar da Habasha da Libyia da Sudan ta Kudu da Uganda.

 

Daraktan yankin Gabas da Kudancin Afirka na hukumar, Mamadou Dian Balde, ya shaida wa manema labarai a Geneva cewa rikicin Sudan shi ne mafi girma da ya raba jama’a da muhallan su a duniya a yanzu.

 

Ya buƙaci ƙasashen duniya su ƙara tallafin kuɗi domin hana ƙara tabarbarewar rayuwar iyalan da rikicin ya raba da muhallan su.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!