Connect with us

Manyan Labarai

Me yasa ruwan sama ke mamaye makarantar Sakandiren Tarauni?

Published

on

Mamamakon ruwan sama da aka wayi gari da shi a yau ya mamaye  kofar shiga makaranatar sakandiren Tarauni dake birnin Kano.

Tashar Freedom radio ta gano cewa ruwan saman na  yau, ya mamaye bakin makarantar sakandiren  ta Tarauni har ta kai ga masu shiga makaranatar ta babbar kofa ,sai kafafuwan su sun shiga cikin ruwa kafin su karasa.

Alamu na nuni da cewa taruwar  ruwa a bakin manyan hanyoyin jahar Kano ya biyo bayan rashin gyara magudanan ruwa da kuma ko in kula daga hukumomi na alkinta ofisoshi mallakar ta.

Makaranatar Sakandiren Tarauni dai ta yi shuhura a yankuna da dama a nan birnin  Kano inda ‘’ya ‘’yan matsaikata ke halattara makarantar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!