Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Filin Mahaha zai koma na Hisbah

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce Gwamnatin Kano zata maida wani bangare na katafaran filin wasa na Mahaha wanda aka fi sani da Takardar tsire, zuwa babbar cibiyar horar da dakarun Hisbah baki daya.

Babban kwmaadan Hisbah na Jihar Kano Sheik Muhammad Harun Ibini Sina ne ya bayyana hakan a yayin da ake tattaunawa da shi ta cikin shirin Shari’a a Aikace na tashar Dala FM da safiyar yau Talata.

Malam Harun Ibini Sina ya ce in har gwamnatin jihar nan ta maida filin wasan na Mahaha za’a yi amfani da shi wajen horar da dakarun Hisbah da koyar da su sana’o’I daban-daban.

Haka zalika babban kwamandan na Hibah ya ce cibiyar za kuma ta taimaka wajen warware matsaloli daban-daban da suka danaganci zamantakewa da kuma sake inganta hukumar zuwa wani mataki.

Yana mai cewar hukumar a halin yanzu na shirin daukar matakai kan kafafan sada zumunta na zamani mussaman wanda ake batanci a cikin su, kasancewar ana yawan samin yaduwar Badala da cikin su.

 

 

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!