Connect with us

Labarai

Ministan kwadago ya sha alwashin fara aiwatar da tsarin mafi karancin albashi

Published

on

Sabon Ministan kwadago da samar da aikin yi, ya sha alwashin tabbatar da cewa, an fara aiwatar da tsarin mafi karancin albashi ga ma’aikatan kasar nan.

 

A jiya Laraba ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin ministoci a zangon mulkin sa na biyu.

 

Da ya ke zantawa da manema labarai a gidan sa da ke Abuja, bayan karbar rantsuwa kama aiki, Dr Chris Ngige, ya ce, samun fahimtar juna tsakanin gwamnati da ma’aikata na daga cikin ayyukan da zai fi  ba da fifiko a wannan karon.

 

Ya ce gwamnati za ta yi iya kokarinta wajen ganin cewa ma’aikatan kasar nan sun kasance cikin walwala a ko da yaushe.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,601 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!