Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Katsina:Jiragen helkwabta ne ke jefo makamai inji wani da ke zargi dan bindiga dadi

Published

on

Wani matashi da ake zargi a matsayin daya daga cikin ‘yan bindiga da suka addabi al’ummar jihar Katsina mai suna Aliyu Musa, ya shaidawa ‘yan sanda cewa, jiragen Helkwabta ne ke jefo musu makamai a dajin Dinya da ke yankin karamar Hukumar Kankara a jihar ta katsina.

 

A cewar sa, tun yana dan kankanin yaro aka ba da shi ga wani makiyayi domin yi mishi kiwo, wanda ya dauke shi zuwa kauyen Dinya.

 

Ya ce a lokuta da dama sun rika shiga gari suna fasa shaguna suna kwashe dukiyoyin jama’a wasu lokutan su sace dabbobi.

 

Ya ce, bayan da sana’ar ta su ta girma, a yanzu, wani jirgin Helkwabta fari ne ke jefo musu makamai da suka hada da: Bindigogi da alburusai, inda mai gidan sa da akewa lakabi da Oga Surajo ya ke kwashesu ya raba musu.

 

Da aka tambayeshi ko ya san wani abu game da jirgin Helkwabtan da ke jefo musu makamai a dajin, ya ce Oga Surajo ne kawai ya san ko su waye masu jirgin Helkwabtan da ke jefo musu makaman.

 

Ya ce a lokuta da dama suna amfani da Babura ne wajen kaiwan hare-haren-inda duk babur ke daukar mutum uku.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!