Connect with us

Kiwon Lafiya

Ministan sufuri ya ce bai ji dadin yarda aikin gina layin dogo da ya tashi zuwa Lagos ke tafiya ba

Published

on

Ministan sufuri Rotimi Amaech  yace bai ji dadin yadda dan kwangilar dake aikin gina layin dogo da ya tashi daga Lagos zuwa badin yake gudanar da aikin sa ba.

 

Rotomi Amaechi yayi mamakin yadda aikin yake tafiyar hawainiy a lokacin da yake ziyarar aiki na wata-wata a jiya kan manyan ayyukan da gwamnatin tarayya ta kaddamar a jiya Talata a birnin Badin.

 

A rahoton da dan kwangilar ya bayar ana zaton cewa zai sauya wa wasu bututun ruwa waje da ya shafi aikin layin dogo, amma kuma ya gazza yin hakan.

 

A cewar Rotomi Amaechi  kamata yayi dan kwangilar ya fara aikin sauyawa bututun da wuri, kamar yadda ya alkawarta amma sai ya gaza yin hakan, bayan da ya ce zai kamamla aikin kafin nan da ranar 2 ga watan Nuwanba mai kamawa, sai dai yawan kawo uziri na rashin aikata hakan

 

Haka zalika ministan na sufuri ya ce alhakin dan kwangilar ne ya  gina tashohin jiragin kasa guda 10 da zai tashi daga Lagos zuwa badin, wanda zai baiwa al’ummar yankin damar yin amfani da tashohin jiragin kasa wajen gudanar da al’amuran yau da kullum.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,434 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!