Labarai
Ministan tsaron Najeriya Badaru Abubakar ya yi murabus

Ministan tsaron Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga muƙaminsa nan take.
Ministan, ya bayyana hakan ne ta cikin wata wasiƙa da ya aike wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana cewa ya yi murabus ne saboda dalilai na lafiyarsa.
Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin nasa, tare da gode masa bisa hidimar da ya yi wa ƙasa.
Ana dai sa ran cewa, Shugaba Tinubu zai sanar da Majalisar Dattawa sunan wanda zai maye Muhammad Badaru Abubakar a cikin makon nan.
You must be logged in to post a comment Login