Labarai
Ministan tsaron ya bukaci a daina biyan kudin fansa ga yan bindiga

Sabon ministan tsaron Najeriya Christopher Musa, ya bukaci mutane da su daina biyan kudin fansa ga masu yin garkuwa da mutane.
Janar Christopher Musa mai Ritaya, ya bayyana hakan ne, bayan da majalisar Dattawa ta kammala tantance shi, tare da tabbatar masa da mukamin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada shi, na ministan tsaro.
Christopher Musa, ya kuma yi alkawarin yin aiki tare da dukkan hukumomin tsaro da jama’a domin magance kalubalen tsaro a fadin Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login