Labarai
Mu na kira ga masu hannu da shunu da su tallafawa matasa-DG Ayyuka na Musamman
Babban Darakta na ayyuka na musamman ga gwamnatin Kano, AVM Ibrahim Umaru (rtd) ya yi kira ga masu hannu da shuni da su mayar da hankali wajen bayar da gudummawarsu ga matasa wajen samar musu da ayyukan yi domin rage zaman banza ga matasan a fadin jihar Kano.
AVM Ibrahim Umaru (rtd) ya yi wannan jawabin ne a lokacin da ya karbi baƙuncin wakilan al’ummar unguwar Madigawa da ke ƙaramar hukumar Dala a lokacin da suka kai masa ziyara a ofishinsa dake fadar gwamnatin Kano.
Ya ce sai an samar da guraben ayyukan yi ga matasa tare da isassun horo kan sana’o’in dogaro da kai, al’umma za ta kubuta daga ci gaba da rashin tsaro da sauran matsalolin da ke kawo illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a bangarori da dama.
“Ina rokon ku da ku kafa kungiyoyin ƙarfafawa matasa a yankunan ku kuma tare da goyon bayan wadanda suke da ƙudirin koyan sana’o’in dogaro da kai. A cewa DG
Tun da fari shugaban kungiyar Alhaji Balarabe Jibrin tsohon mataimakin magatakarda na majalisar dokokin jihar Kano ya ce sun zo ofishin Daraktan ne domin jin irin gudunmawar da ya bayarwa wajen ci gaban Madigawa da ƙaramar hukumar Dala dama jih baki daya.
Alhaji Balarabe ya yaba da irin gudunmawar da Daraktan yake bayarwa wajen samar da tsaro a jihar, inda ya yi alkawarin ci gaba da gudanar da addu’o’i ga dukkanin al’ummar Madigawa ga Darakta Janar da kuma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf domin samun zaman lafiya da ci gaban jihar.
You must be logged in to post a comment Login