Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun Baiwa Kamfanin KEDCO Wa’adin Mako Hudu Da Ya Samar Da Wuta A Yankin Unguwar Sallari Dake Kano: NERD

Published

on

Hukumar kula da samar da wutar lantarki ta kasa reshen jihar Kano NERC ta baiwa kamfanin rarraba wutar lantarki wa’adin mako hudu da ya samar da wuta a yankin unguwar Sallari Babban Giji.

Umarnin na zuwa yayin da kungiyar ci gaban unguwar Sallari babban Giji ta kai korafi hukumar ta NERC kan yadda suka shafe sama da shida suna fuskantar matsalar rashin wuta wanda hakan ke jawo musu koma baya a al’amuran su na yau da kullum.

Tawagar kungiyar karkashin shugaban kungiyar Abdumajid Abubakar Sadiq ya bayyana irin matsalolin da suke fuskanta.

Yayin da suke karbar korafin jami’an hukumar ta NERC sun bayyana cewa za su yi duk mai yiwuwa wajen kawo karshen matsala rashin wula a yankin na Babban Giji, har ma suka baiwa kamfanin na Kedco wa’adin sati hudu domin samar da wuta a yankin ko kuma su dau matak a kan su.

Sai dai ba su yadda mun nadi muryarsu ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!