Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun bawa sarakuna wa’adin awanni 48 da su kwashe kayan su – Gwamna Abba

Published

on

Biyo bayan sanya hannu akan takardar cire sarakuna da Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf yayi, Gwamnan ya bawa sarakuna wa’adin awannin 44 da su kwashe kayan su daga gidan gwamnati domin yanzu haka sarki ɗaya ne a jihar kano, inda gwamnan ya tabbatar da dawo da Sunusi lamido sunusi na biyu a matsayin sabon sarkin jihar Kano inda yace ancire shi ne ba bisa ƙaƙida ba.

Gwamna Abba Kabir Yusuf yayi wannan jawabin ne da yammacin yau Alhamis yayin taron manema labarai da ya gudanar a fadar gwamnatin Kano domin tabbatar da dawo Sunusi lamido Sunusi kujerar sa.

Gwamnan ya kuma ce la’akari da yadda zaka zartar da hukuncin a wance lokacin ba bisa ƙaƙida ba shiyasa akayi duba akan hukuncin domin tabbatar anyi abinda ya dace.

Haka kuma gwamnan ya tabbatar da cewa yanzu haka a jihar Kano sarki ɗaya ne babu wani sarki sai Sunusi lamido *Sunusi.

Gwamnan ya shawarci sauran sarakunan da aka cire da su tabbatar sunyi biyayya da umarnin da aka basu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!