Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Barka Da Hantsi

Mun gina makarantu ɗari 3 a Jigawa – Dakta Lawan Ɗanzomo

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ya zuwa yanzu ta gina makarantun furamare da na sakandare guda ɗari 3.

Samar da makarantun wani mataki ne na inganta harkokin ilimi a fadin jihar.

Kwamishinan ilimi Dakta Lawan Yunusa Ɗan Zomo ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala shirin “Barka da Hantsi” na Freedom Radio.

Dakta Lawan Yunusa Ɗan Zomo ya ce yanzu haka gwamnatin jihar na ƙara aikin tantance malaman makarantun firamare da na sakandare a ƙananan hukumomin jihar domin tabbatar da kyakkyawan tushen ilimi.

“Cikin matakan da muke bi domin farfaɗo da harkar ilimin sun haɗar da shiga inda fulani makiyaya suke domin su ma a basu gudunmawa ta fannin ilimi a fadin jihar”.

Dakta Lawan Yunusa Ɗan Zomo ya ce, a yanzu gwamnatin jihar tana bai wa matasa da suke da ƙwazo a fannoni daban daban na rayuwa aikin yi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!