Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Son zuciya: Matasa sun yi garkuwa da yaro a Kano

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da kuɓutar da wani yaro ɗan shekara 3 da aka yi garkuwa da shi a Kano.

Mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio.

Kiyawa ya ce ” ranar 24 ga watan 8 mun samu ƙorafi daga wani bawan Allah da ke zaune a unguwar Ja’een a nan Kano, kan cewa an yi garkuwa da ɗan sa kuma an nemi ya biya kuɗin fansa naira miliyan 10 wanda daga baya aka yi masa ragi zuwa dubu ɗari 6″.

DSP Kiyawa ya ce, bayan ƙorafin ƴan sanda sun samu nasarar kama wasu mutane 2 da suka haɗar da Ashiru Yakubu mai shekara 22 da Abdullahi Mukhtar mai shekara 20 a unguwar Ja’een waɗanda su ne suka sace shi.

“Binciken farko sun tabbatar da cewa su suka sace yaron ɗan shekara 3 mai suna Muhammad Aminu, kuma za mu ci gaba da bincike don gano yadda lamarin ya faru”.

Kiyawa ya gargaɗi jama’a da su san Mutanen da za su riƙa mu’amala da su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!