Labarai
Mun kama masu Garkuwa da mutane da barayin baburan – Dikko
Rundunar yan sandan jihar Kano ta yi holin wasu mutane da ta kama bisa zargin laifin fashi da makami tare da garkuwa da mutane.
Baya ga wannan ma ana zargin mutanen da satar motoci da baburan Adaidaita sahu da babura masu kafa biyu sai Kuma masu safarar miyagun kwayoyi.
Kwamishinan yan sandan Kano Samaila Shu’aibu Dikko ne ya tabbatar da hakan a zantawarsa da Freedom Radio.
Ya ce mutanen da aka kama an same su da bindigogi da magungunan da amfaninsu ya kare.
Dikko ya yabawa jami’an tsaro da yan jaridu bisa gudunmawar da suke bayarwa, inda ya tabbatar da cewa da zarar an kammala bincike za a tura su kotu don a yanke musu hukunci.
You must be logged in to post a comment Login