Labarai
Mun kusa kawo karshen rikicin cikin gida a PDP – Turaki

Daya daga cikin bangarorin jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki ya tabbatar da fara sabon yunkurin sulhu domin hada kan bangarorin da ke rikici a cikin jam’iyyar.
A wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa, Turaki ya ce shugabannin jam’iyyar na nazarin hanyoyi daban-daban da za su kai ga samun dawwamammen zaman lafiya a cikin PDP.
Ya bayyana cewa wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin rage sabani da rarrabuwar kawuna da suka dabaibaye jam’iyyar a ‘yan kwanakin nan.
You must be logged in to post a comment Login