Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun magance korafi fiye da 500 a bana- KIRS

Published

on

Hukumar tattara haraji ta jihar Kano ta ce ta magance korafi fiye da Dari biyar ciki korfe-korafe kimanin Dari shida da suka shafi alamuran karbar haraji a jihar kano daga farkon shekarar 2023 zuwa yanzu.

Mai magana da yawun hukumar Rabiu Sale Rimin Gado, ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan haraji da ya gudana a ofishin hukumar da hadin guiwar Kungiyar tabbatar da Adalci wajen karba da sarrafa harani wato Taxs Justice and Government platform.

Rimin Gado ya kuma kara da cewa ‘akwai sashin da suka samar na zamani da zai rika sauraron korafin masu biyan haraji dan magance korafe-korafe cikin sauki.

Rabi’u Sale Rimin Gado ya kuma ce, ‘akwai hanyoyin samun duk bayanin da masu biyan haraji ke bukata na zamani ko zuwa kafa da kafa dan shigar da korafi ko samun bayani.

A nasa jawabin Shugaban kungiyar ta Taxs Justice and Government platform dake rajin tabbatar da adalci wajen karba da sarrafa harajin ta kasa reshen jihar Kano Dr Muhammad Mustapha Yahya, ya ce ‘kungiyar na taimakawa ne wajen wayar da kan Al’umma Muhimmancin biyan haraji da kuma tabbatar da ganin anyi abunda ya kamata da harajin.

Yayin taron an kuma tattauna hanyoyin da za a saukakawa masu biyan haraji da samar da ayyukan cigaban al’umma a fanin lafiya, Ilimi, kasuwanci da tsaro a fadin jihar.

Rahoton: Abba Isa Muhammad

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!