Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun rushe hukumar REMASAB – Ganduje

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da rushe hukumar kwashe shara ta jihar REMASAB.

Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da Freedom Radio.

Ya ce, “gwamnatin Kano ta rushe hukumar, sai dai babu wani ma’aikaci ɗaya da zai rasa ayikin sa, domin kuwa an yi tsarin rarraba ma’aikatan hukumar zuwa wasu hukumomin, su kuwa ma’aikatan wucin gadi mun mikawa kamfanin su, su yi aiki tare” a cewar Getso.

Ya ce, tuni gwamnati ta dauki matakin sauya salon sarrafa shara ta hanyar hadin guiwa da wani kamfani mai zaman kan sa da zai rika sarrafa shara, don ta zamo takin zamani da iskar gas da kuma wutar lantarki.

“kamfanin zai rika biyan gwamnati naira miliyan 50 a shekarar farko, a shekara ta biyu za su biya miliyan 100, haka zalika a shekara ta uku za su biya naira miliyan 200” inji kwamishinan muhalli.

Getso ya kuma ce, kamfanin zai ɗauki ma’aikata sama da dubu hudu ciki har da injiniyoyi, kuma za su ninka albashin ma’aikatan da aka basu har sau uku.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!