Connect with us

Labarai

Mun samar wa maniyyata 1,010 Visa- Gwamnatin Yobe

Published

on

Hukumar kula da jin dadin alhazai ta Jihar Yobe, ta bayyana cewa, ta yi wa maniyyata dubu daya da goma Bizar shiga kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana cikin maniyyatan jihar dubu daya da casa’in da hudu.

Shugaban hukumar Alhaji Mai Aliyu Usman, ne ya bayyana hakan a zantawarsa da wakilinmu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim.

Shugaban, ya yi karin bayani game da shirin su na tunkarar ibadar aikin Hajjin mai zuwa, inda ya bayyana cewa,  sun kuma tanadi Dalolin Amurka da za su bai wa kowane maniyyaci kudin guzuri domin shirin gudanar da aikin Hajji bana.

Alhaji Mai Aliyu Usman, ya kara da cewa, sun sayi Dalar ne daga wani kamfanin canjin kudaden ketare, inda za su bai wa kowanne maniyyaci Dala 500.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!