Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun umarci sarakuna su kama aiki nan take- Gwamna Abba

Published

on

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya naɗa sababbin sarakuna masu daraja ta biyu a jihar.

Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da babban daraktan yaɗa labaran Gwamna Alhaji Sunusi Bature Dawakin tofa ya fitar ya tabawa manema labarai

Waɗanda aka naɗa ɗin su ne Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya, a matsayin Sarkin Gaya, wanda kafin naɗinsa shi ne tsohon Sarkin Masarautar Gaya da aka rushe.

Sai Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, a matsayin Sarkin Karaye, wanda kafin naɗinsa shi ne hakimin Rogo.

Sai kuma Alhaji Muhammad Isa Umar, a matsayin Sarkin Rano, wanda kafin naɗinsa shi ne hakimin Bunkure.

A cikin sanarwar da aka fitar naɗin zai fara aiki nan take.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!