Labarai
Muna da ƙwarin gwiwar kammala duk ayyukan Kilomita 5- Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce, ta na da kwarin gwiwa na kammala aiyyukan Titunan kilomita biyar da ke fadin jihar nan kafin cikar wa’adin watan Disamba da aka saka na gama aiyyukan.
Aiyyukan wanda suka kunshi Titunan kilomita biyar na kananan hukumomin Kura da Garun Malam sai Rano, da a baya aka karbe daga hannun ‘yan kwangilar dake aiwatar da su sakamakon tsaiko da kin tafiyar aikin da a yanzu haka aikin ya kai kaso 95, kamar yadda ma’aikatar bibiyar aiyyukan gwamnatin jiha ta tabbatar.
Da yake jawabi ga tawagar kwamishinan ma’aikatar bibiyar aiyyukan ya yin ziyarar duba aiyyukan da yadda suke gudana a karamar hukumar Garun Malam , wakilin dagacin garin Malam Halilu Sani Turaki, ya yi karin haske kan aikin tare da yabawa gwamnatin jihar Kano.
Da yake nashi Jawabin Kwamishinan ma’aikatar Kwamred Nura Iro Ma’aji Sumaila, ya bukaci ‘yan kwangilar da su tabbatar da kammala aiyyukan akan lokacin da aka kayyade na watan Disamba.
A ziyarar duba aiyyukan Kwamred Nura Iro Ma’aji Sumaila, ya duba aikin dake tafiya na Bebeji da Bunkure sai Asibitin Garun Malam da aka daga Darajar sa daga Karami na Sha ka tafi zuwa babba.
You must be logged in to post a comment Login