Labarai
Muna gudanar da bincike kan yadda Breaker ya saki sabuwar waƙa- Gwamnatin Kano

Hukumar tace Fina-finan da Dab’i ta Jihar Kano, ta ce tana kan gudanar da bincike domin gano yadda mawaki Hamisu Breaker ya saki sabuwar wakarsa mai suna Amanata ba tare da hukumar ta tantance ta ba.
Mai magana da yawun hukumar Abdullahi Sani Sulaiman, ne ya bayyana hakan ta cikin wani sakon murya da ya aiko wa Freedom Radio a yau Alhamis.
Abdullahi Sani Sulaiman ya ce, aikin dakatar da wakar ba na hukumar Hisbah ba ne, na hukumar tace fina-finai ne, amma ba laifi bane don hukumar Hisbah ta magantu a kai domin kuwa suna aiki kafada da kafada.
You must be logged in to post a comment Login