Labarai
Muna kan bakar mu na karɓar Haraji a hannun ƴan adaidaita – Mahmud Santsi
Gwamnatin jihar Kano ta ce, tana kan bakar ta na karɓar kuɗaɗen haraji da ta saba karɓa a hannun matuƙa baburan adaidaita sahu.
Kwamishinan sufuri da gidaje Mahmud Santsi ne ya bayyana hakan a zantawar sa da wakiliyar Freedom Radio Zahra’u Nasir ta wayar tarho.
Santsi ya ce, matuƙar matuƙa baburan adaidaita sahun za su ci gaba da aiki a Kano to kuwa sai sun biya kuɗaɗen da aka ƙayyade musu.
Ko da aka tambaye shi kan makomar al’umma na yin zirga zirga kasancewa an dogara da yin sufuri a cikin baburan adaidaita sahu, Kwamishinan ya ce “Tuni muka kira kamfanin mu na zirga-zirga Kano line da ke sufurin al’umma zuwa sassan ƙasar nan da su dawo gida su ragewa al’umma raɗaɗin rashin abin hawa”.
“Gwamnatin jihar Kano ta bai wa kamfanin nan da yake son harkar sufuri a Kano mai motocin Safa Safa guda 12 wanda tuni dama gwamnati ta basu kwangilar kawo motocin guda 100 yanzu haka mun bada umarnin guda 12 su fito su fara aikin sufurin jama’a”.
A cewar Santsi, tuni motocin sun fara aiki tun daga yau Talata, kuma akwai buƙatar sauran masu ababen hawa a Kano da su riƙa taimakawa al’umma wajen rage musu hanya zuwa guraren harkokin su na yau da kullum.
Har ma ya bai wa al’ummar jihar Kano haƙuri tare da shan alwashin kawo ƙarshen matsalar gaba ɗaya, don kuwa shirin samar da tsarin “Bus Masa Transit” yayi nisa wanda zai magance faruwar matsalar sufuri a Kano.
Kwamishinan ya ce, tsarin ba zai hana masu baburin adaidaita sahu su ci gaba da kasuwancin su a jihar Kano ba.
You must be logged in to post a comment Login