Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Muna kira ga ƙungiyoyin ci gaban Arewa da su haɗa kansu – Sarkin Kano

Published

on

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya buƙaci ƙungiyoyin da ke rajin kawowa Arewacin Najeriya da su haɗa kansu guri guda domin kawowa yankin ci gaba ta kowane ɓangare.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan a ranar Lahadi, yayin taron Walimar taya Wazirin Dutse Alhaji Bashir Muhammad Dalhatu murnar naɗin da aka yi masa na shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar tuntuba ta Dattawan Arewa ACF.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya ƙara da cewa bai kamata ace ƙungiyoyin dake rajin kawowa yankin Arewacin ƙasar na ci gaba suna faɗa da junansu ba ta hanyar yin sa’insa a kan wani maudi’i, domin hakan babbar matsala ce ga ci gaban yankin.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa, taron walimar ya samu halartar Sarakuna daga ko’ina a faɗin Najeriya da sauran manyan ‘yan kasuwa da masu ruwa da tsaki na gwamnati a kowane matakai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!