Labarai
Muna kira ga Alhazai su ƙauracewa ɗaukar kayan da ƙasar Saudiyya ta hana shiga da shi-Gwamnan Kano
Gwamnatin jihar kano ta yi kira ga alhazan bana da su ƙauracewa ɗaukar duk wani abu da ƙasar Saudiyya ta haramta shiga da shi ƙasar domin kaucewa faɗawa fushin hukumar ƙasar.
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ne yayi wannan jawabin a yau yayin kammala taron bita da akeyiwa maniyata aikin Hajjin bana domin tunatar da su yadda zasu gudanar da aikin hajjin su yadda addini ya tanadar.
Gwamna Yusuf ya kuma tabbatar wa da alhazan jihar cewa gwamnati zata basu duk wata gudunmawa da ake bayarwa ga alhazan a ƙasa mai tsarki.
Da yake jawabi shugaban hukumar alhazai na jihar Kano Alhaji Lamin Rab’u Dan Baffa ƙarin haske yayi kan irin tsare-tsaren da sukayi wajen gudanar da aikin hajjin bana
Lamin ya kuma ce sun fara wannan bitar ne tun cikin azumi domin ƙara wayarwa da alhazai kai a fannin yadda zasu gudanar da aikin su a ƙasa mai tsarki.
Haka kuma mun samar da masana fannin harkar gudanar da aikin hajji domin suyiwa alhazan bana bita kan yadda ake aikin hajji da irin ƙaƙidojin da ake bi wajen aikin.
Muna kira ga alhazai da su tabbatar sun zamto jakadu na gari wajen gudanar da aikin su yadda ya kamata A cewar Gwamnan.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya buƙaci alhazan da zasu tafi zuwa ƙasar ta Saudi Arabia da su kasance masu yiwa jihar Kano addu’a dama ƙasa baƙi ɗaya domin samin ci gaba a dukkanin ɓangarori.
You must be logged in to post a comment Login