Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsadar rayuwa: Ƴan kasuwar Kwari sun nemi ɗaukin Ubangiji

Published

on

Shugabancin kasuwar Kwari ya gudanar da Sallah da addu’ar neman saukin matsin rayuwa da ake fama da shi domin samin sassauci.

Shugaban kasuwar Alhaji Hamisu Sa’adu Dogon Nama ne ya jagoranta inda ya buƙaci dukkanin ƴan kasuwar da su mayar da hankali wajen roƙon Ubangiji kan yadda halin matsin a ko wanne ɓangare na rayuwa, inda suke kira ga ƴan kasuwar da suma su samar da sauki a kayan da suke shiyarwa.

Alhaji Hamisu Sa’adu Dogon Nama ya kuma ƙara da cewa zasuyi duk mai yihuwa wajen ganin sun samar da tsarin da zai sauƙaƙawa al’umma musamman masu zuwa kasuwar su ta kwari domin samin daidaiton farashi.

Ya ƙara da cewa yanzu haka sun sami sahalewa gyara filin idi domin ajiye ababan hawa da kuma lodi.

Dogon Nama ya kuma ce dole sai ƴan kasuwar suma sun kiyaye musamman yadda a tsakanin su shuke ajiye kaya akan hanya wanda haka ke bayuwa ga tushewar kasuwar.

Shugabancin kasuwar yace zai dau mataki ga duk wani ɗan kasuwa da ta samu da karya dokar kasuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!