Labarai
Muntari Ishaq Yakasai ya ajiye Kwamishina domin takarar majalisar tarayya
Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Kano Alhaji Muntari Ishaq Yakasai ya sauka daga muƙaminsa don takarar ɗan majalisar tarayya a Ƙaramar hukumar Birni.
Mai taimakawa Gwamnan kan kafafen sada zumunta Abubakar Aminu Ibrahim ne ya sanar da hakan ta shafinsa na Facebook.
Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da Gwamna Ganduje ya bai wa masu riƙe da muƙaman siyasa da ke sha’awar takara umarnin ajiye aiki domin biyayya ga dokar zaɓe.
Kawo yanzu Kwamishinoni biyar ne suka ajiye muƙamansu a yau, tare da wasu daga hadiman Gwamnati da zimmar tsayawa takara.
You must be logged in to post a comment Login