Connect with us

Kiwon Lafiya

Mutane 11sun rasa rayukansu sakamakon hatsarin mota a titin Ibeto zuwa Kontagora

Published

on

Mutane goma sha daya sun rasa rayukansu sakamakon mummunan hatsarin mota da ya ritsa da su akan titin Ibeto zuwa Kontagora a jihar Niger.

Babban jami’in hukumar kare abkuwar hadurra ta kasa shiyyar Kontagora Malam Abdullahi Ibrahim, ya shaidawa manema labarai cewa hatsarin ya ritsa da mutane 27 ne yayin da wasu goma sha shida suka jikkata.

A cewar sa, wasu motoci biyu ne su ka yi taho mu gama wanda dayan ke hanyar tafiya birnin Kebbi a jihar Kebbi.

Jami’in hukumar ta FRSC ya alakanta abkuwar hatsarin da tukin ganganci, inda ya shawarci direbobi da su rika kula da yadda su ke tuki.

Ya kuma ce tuni aka garzaya da gawawwakin da wadanda suka jikkata zuwa babban Asibitin Kontagora.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,749 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!