Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta NECO ta saki sakamakon jarrabawar na bana

Published

on

Hukumar shirya jarrabawar kammala makarantun sakandire ta kasa NECO ta saki sakamakon jarrabawar da daliban kasar nan suka rubuta tsakanin watan Yuni da Yulin bana.

A cewar hukumar ta NECO, sama da kaso 71 na daliban sun samu kiredit 5 da suka hadar da darusan Turanci da Lissafi.

Mukaddashin shugaban hukumar Abubakar Muhammad Gana ne ya bayyana hakan ga manema labarai yau a garin Minna, ya na mai cewa ci gaban da aka samu bai kai kaso daya cikin dari ba, idan aka kwatanta da shekarar bara.

Kamar yadda ya bayyana dalibai sama dubu dari 8 da 75 cikin miliyan daya da suka zauna jarrabawar sun samu kiredit 5 ciki babu darasin lisaffi dana turanci, inda kuma wadanda suka samu kiredit 5 da suka hadar da Turanci da Lissafi suka kai kaso 82 cikin dari.

Abubakar Muhammad Gana ya kuma ce akwai matsalolin satar Jarrabawa da suka samu sama da dubu 20, inda yace sun kama dalibai sama da dubu bakwai da suke satar amsa daga littattafai, inda ya ce an fi samun matsaloli a darasin Lissafi sama da kowanne darasi sai kuma darasin Turanci.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!