Labarai
Mutane 20 sun rasu sakamakon kifewar jirgin ruwa

Mutane 20 sun rasu yayin da aka ceto 13 da sakamakon kifewar wani jirgin ruwa da ya tashi daga Adiyani a Karamar Hukumar Guri ta Jihar Jigawa zuwa Nguru a Jihar Yobe.
Wani shaidar gani da ido mazaunin garin Nguru ya bayyana cewa, har yanzu ana ci gaba da neman wasu mutane 15 da ake zargin sun nutse cikin ruwan, yayin da jami’ai ke gudanar da ayyukan ceto da bincike a yankin.
Hatsarin, wanda ya faru da misalin karfe 7 na daren jiya Asabar, ya jefa al’ummar yankin cikin jimami, yayin da mazauna ke bai wa jami’an ceto goyon baya a kokarin gano sauran mutanen da ake fatan cetowa ko gano gawarwaki.
Mazauna yankin na ci gaba da zaman dar da damuwa da rashin tabbas game da wasu ‘yan uwansu da ke cikin jirgin, yayin da hukumomi suka yi kira ga jama’a da su kiyaye hanyoyin ruwa da bin ka’idojin Tuki.
You must be logged in to post a comment Login