Labarai
Mutane 371 aka kashe a Zamfara daga watan Janairu zuwa yanzu-Amnesty International
Kungiyar kare hakkil bil’adama ta Amnesty International ta ce mutane 371 aka kashe a Jihar Zamfara daga watan Janairun bana zuwa yanzu, sannan daruruwan mutane suka bar gidajensu sakamakon hare-haren ‘yan bindiga.
Mai magana da yawun kungiyar a Najeriya Isa Sanusi ne ya sanar da hakan cikin sanarwar ya bayar a jiya, yana mai cewa tashe-tashen hankula a Jihar na ci gaba da kamari sakamakon yawaitar kashe-kashen mutane da kuma garkuwa da su da ake faman yi.
Ya ce dubban mutane ne suka bar gidajensu tun bayan fara rikicin a cikin shekarar 2012 biyo bayan fadace-fadace tsakanin Makiyaya da Manoma, inda ya ce daraktan kungiyar a kasar nan Osai Ojigho ya yi zargin cewa halin ko in kula daga bangaren mahukunta ne ya sanya al’amarin ya yi kamari.
Amnestin ta ce ko ranar 27 ga watan Yulin jiya sai da ‘yan bindigar suka farwa kauyuka 18 a garuruwan Mashema da Kwashabawa da kuma Birane a karamar hukumar Zurmi, tare da hallaka mutane 42.
Akalla dai mutane dubu goma sha takwas ne dai suka bar gidajensu don neman mafaka sakamakon hare-haren ‘yan bindigar a Jihar Zamfara.