Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mutane 9 sun rasu sakamakon faɗawar Mota cikin ruwa a garin Gwarzo

Published

on

Hukumar kashe gobara ta Kano ta tabbatar da rasuwar mutane 9 a wani ibtila’in faɗawar Mota cikin ruwa.

Lamarin ya faru ne a daren Asabar, daidai Dam ɗin Fada da ke dab da shiga garin Gwarzo, inda motar ƙirar Golf ta kauce hanya ta faɗa ruwan.

Kakakin hukumar kashe gobara na Kano Saminu Yusuf Abdullahi ya ce, motar ta taso ne daga Kano zuwa Katsina.

Ya ce, hatsarin ya faru ne sakamakon fashewar tayar motar.

An ceto mutane 12, amma 9 daga ciki sun rasu a asibitin garin Gwarzo, yayin da 3 ke ci gaba da samun kulawa.

Ana kuma ci gaba da neman ceto mutum guda a ruwan.

Mutanen da ke cikin motar sun hada da manya mata da maza sai kuma kananan yara ƴan kimanin watanni 6.

Hukumar kashe gobarar ta Kano ta ce ta yi aikin ceton ne tare da tallafin Masuntan da ke yankin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!