Connect with us

Labarai

Mutanen da suka rasu a fashewar tankar mai a Neja sun ƙaru zuwa 45

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta ce adadin waɗanda suka rasu a sanadiyar fashewar tankar man fetur a babban titin Bida zuwa Agaie a ƙaramar hukumar Katcha na jihar Neja sun ƙaru zuwa 45.

Hukumar ta ƙara da cewa zuwa yanzu akwai kusan mutum 63 da suke ci gaba da jinyar raunukan da suka samu, kamar yadda babban jam’in hukumar na shiryar jihohin Kwara da Neja ya bayyana wa tashar Channels a ranar Juma’a.

Ya ce mutane 45, maza 12 mata 27, suka rasu  sannan a akwai ƙananan yara guda shida. A ɓangaren waɗanda suka jikkata kuwa akwai kusan mutum 63, maza 24 mata 32 da ƙananan yara shida,” in ji shi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!