Labarai
Mutanen garin Bakalari sun koka kan masu kwasar Bahaya
Al’ummar Kauyen Bakalari da ke yankin karamar hukumar Tofa a nan Jihar Kano, sun koka dangane da yadda wasu mutane ke jibge musu bahaya da suke kwasowa daga bangarori daban-daban na jihar Kano.
Jama’ar garin sun ce, wannan lamari dai, yana shafar lafiyar su dana iyalansu har ma dana dabbobinsu.
Har ila yau mazauna garin sun ce ya dau tsawon lokaci yana faruwa, inda masu kwasar bahayan ke debo shi daga cikin birni su kawo yankinsu su jibge sannan su busar da ita.
A cewar su bayan sun busar da bahayar, sai kuma su rika durawa a buhu suna sayarwa, wanda hakan kan haifar musu da cututtuka da dama.
Malam Safiyanu Idris Ramosin, shine shugaban masu sana’ar busar da bahaya a kauyen na Bakalari, ya shaidawa wakiliyar mu Maryam Muhammad Bawa cewa, sun dade suna wannan sana’a kuma al’ummar garin basu taba yi musu korafi akai ba sai wannan karon.
Mallam Safiyanu ya kara da cewa sama da mutane 200 ne ke samun rufin asiri ta hanyar wannan sana’ar tasu.
A nasa bangaren Mai Garin Janguza, Malam Hudu Ya’u, ya ce, shi abin yafi karfin sa, saboda masu aikin ba-hayar sune suka sayi filin da kudinsu.
Har ila yau, wakliyar mu Maryam Muhammad Bawa ta tunubi sarkin tsaftar jihar Kano, Alhaji Ja’afaru Ahmed Gwarzo wanda ya ce duk da yake gwamnati ce ta samar da wurin don gudanar da wannan sana’a, amma yadda su ke aikin, bai dace ba.
Freedom Radio ta tuntubi ma’aikatar muhalli ta jihar Kano kan wannan batu, inda mataimakin daraktan kula da gurbacewar muhalli a ma’aikatar Muhammad Baba Ahmad ya ce, akwai irin wadannan wurare guda hudu da gwamnati ta ware, sai dai an tsara gudanar da wasu ayyuka kafin fara gudanar aiki a wuraren
Alhaji Muhammad ya kuma ce nan ba da dadewa ba, mai’akatar za ta yi duk me yiwuwa domin daukar matakin dakile matsalolin gurbacewar muhallin da ke addabar al’ummar garin na Bakalari da ke kusa da Mahuwa sakamakon jibge bahayar.
You must be logged in to post a comment Login