Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Rahotonni

Yadda al’ummar Dawakin Kudu suka koka kan matsalar hanya

Published

on

A kwanan nan ne wasu al’ummomin garuruwan Dantube da Tasa da wasu kauyuka da ke makwabtaka da su a yankin karamar hukumar Dawakin Kudu a nan jihar Kano, su ka koka kan cewa wani mutum ya toshe musu titin shiga kauyukan na su.

Mutanen wadanda suka garzayo nan gidan Rediyo Freedom da koken na su, sun ce sun yi iya kokarinsu domin ganin ba a toshe musu titin ba, wanda suka ce bankin duniya ne ya gina shi shekaru da dama da suka gabata.

Malam Jamil Sani Paki, daya daga cikin mutanen da suka yi korafin cewa mutumin mai suna Jamilu Haruna Soja ya gine hanya daya tilo da ake amfani da ita wajen shiga kauyen Dantube, wanda ya ce ya yi hakan ne domin samun isash-shen fili a wata jami’a da yake ginawa.

A cewarsu tun farko sun tuntube shi don sanin makasudin toshe titin, sai dai ya tabbatar musu da cewa za a yi hakan ne da nufin hana masu manyan motocin daukar yashi wucewa, inda kuma ya bude wani titin na daban kusa da wani Dutse da suka ce ba su gamsu da shi ba, kamar yadda Malam Ali Hassan, daya daga cikin masu korafin ke cewa.

Sai dai yayin da muke kokarin jin ta bakin mutumin da ake zargi kan wannan batu wato Alhaji Jamilu Haruna Soja, sai labarin ya sauya, sakamakon lashe amai da masu korafin suka yi, wato al’ummomin garuruwan na Dantube da Tasa, wadanda tun farko suka gabatar da wani shiri a daya daga cikin gidajen rediyo masu zaman kansu dake nan Kano kan wannan batu.

Abdulmudallib Ahmad Muhammed, shi ne limamin Masallacin Iqra, wanda ya yi magana a madadin Jamilu Haruna Soja, ya ce tun farko rashin fahimta aka samu har maganar ta kai haka.

Yanzu haka dai bangarorin biyu dai cimma sulhu kan wannan lamari, sannan sun kuma yabawa gidan Rediyo Freedom sakamakon kokarin tuntubar ko wane bangare domin tabbatar da adalci a cikin batun.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!