Labarai
Mutuwar wani: Kasuwar ƴan ƙurƙura ta buɗe a Kano
Yajin aikin matuƙa babura masu ƙafa uku da aka fi sani da Adaidai sahu a Kano ya buɗe ƙofar cin kasuwar masu motocin ƙurƙura.
Tun bayan da aka wayi gari da yajin aikin direbobin ne, aka lura da yadda masu ƙurƙurar ke jigilar mutane zuwa guraren da suka nufa.
Lamarin dai ya zamo sabo domin kuwa ba a saba ganin jigilar mutane a irin waɗannan motoci ba, wanda kuma a yanzu sai ga shi ana yi, har da yin lodin fasinjojin da suka wuce ƙa’ida.
Rashin baburin adaidaihu a wannan rana ya tilastawa wasu daga cikin mutane hawa motocin domin samun isa wuraren ayyaukan su.
Dama dai tuni matuƙa baburan adaidaita sahun suka yi barazanar tsunduma yajin aikin, don nuna damuwar su kan yadda hukumar KAROTA ta tilasta musu sauya lamba da kuma takardun lasisin tuƙi.
Wanda hakan ya jefa zullumi da fargaba a zuƙatan al’umma, kasancewa direbobin sun taɓa tafiya yajin aiki a shekarar 2021.
You must be logged in to post a comment Login