Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Yadda zanga-zangar kawo karshen yajin aikin ASUU ta mamaye wasu jihohin Najeriya

Published

on

Shugabannin kungiyar kwadago ta NLC

Tun da safiyar yau ne daruruwan al’umma da suka fito daga kungiyoyin daban daban suka fito domin gudanar da zanga-zangar lumana.

Cikin kungiyoyin kuwa sun hada da na kwadago NLC hadin gwiwa da sauran kungiyoyin kwadago da na jami’o’in kasar nan har ma da na dalibai.

Cikin jihohin da suke gudanar da zanga-zangar akwai Kano, da Jigawa da kuma Kaduna.

Tawagar masu zanga-zanga

A Kano dai kungiyoyin dun fito zanga-zangar ne dauke da kwalaye masu rubutu a jiki wanda ke nuna bukatar a sauke ministan ilimi Adamu Adamu da kuma ministan kwadago da samar da aikin yi Chris Ngige.

Yayin da wasu rubutun dabke dauke a sauran kwalayen ke nuna halin da daliban jami’o’in kasar nan suke ciki sakamakon yajin aikin kungiyar ASUU.

Tun da sanyin safiyar yau Talata ne gamayyar kungiyoyin suka yi dafifi a shataletalan Mundubawa da ke Bompai wanda daga nan suka garzaya zuwa gidan gwamnatin Kano.

Yadda zanga-zangar ta kasance

Cikin shugabannin tawagar zanga-zangar akwai shugaban kungiyar kwadago NLC na Kano Kwamared Kabiru Ado Minjibir wanda ya tabbatar da cewa” matukar ba a kawo karshen yajin aikin ASUU ba, mu ma za mu tafi yajin aikin gargadi na kwana 3 daga nan kuma mu shiga wanda sai Baba ta gani.

A bangaren dalibai ma sun koka kan yadda yajin aikin ya dakatar musu da karatunsu tsawon wata 6.

Zanga-zangar dai an shirya ta ne don nuna bacin rai kan yadda aka gaza samar da daidaito tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU kan yajin aikin da suka shiga tun a watan Fabrairun 2022.

Yanzu haka dai an shafe tsawon watanni 6 ana yajin aikin bisa zargin da ASUU ke you gwamnatin tarayya na rashin biyan bukatunta.

Haka kuma a halin yanzu wasu jihohin suma na ci gaba da gudanar da zanga-zangar lumana don nuna halin da suke ciki ga hukumomin da abin ya shafa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!