Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Na amince a riƙa ɗaukan jami’an ƴan sanda dubu 10 duk shekara don yaƙi da matsalar tsaro – Buhari

Published

on

Shugaban kasa muhammadu Buhari ya ce rundunar yan sandan kasar an na da damar daukar sabbin jami’ai guda dubu goma duk shekara domin yaki da ayyukan ta’addanci.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabin taya al’ummar Najeriya murnar cika shekaru sittin da daya da samun yancin kai.

Muhammdu Buhari ya yabawa jami’an tsaron kasar nan maza da mata bisa yadda suke jajircewa wajen yaki da ayyukan bata gari a Najeriya.

Shugaban kasar ya ce jajircewa da Jami’an tsaron suke yi na yaki da ta’addanci ne ya sanya da yawa daga cikin mayakan boko haram suka zubar da makamansu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!