Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Na faɗawa Buhari zan tsaya takara ta shugaban ƙasa a 2023 – Tinubu

Published

on

Uban jam’iyyar APC na ƙasa Asiwaju Bola Tinubu ya ce, yaje wajen shugaba Buhari ne domin ya sanar da shi cewa zai tsaya takara a shekarar 2023.

Asiwaju Bola Tinubu ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala wata ganawar sirri da yayi da shugaba Buhari a fadar sa da ke Villa a Abuja.

Ya ce, ta hanyar sanar da shugaba Buhari ne, ƴan Najeriya za su san ƙudurin sa na tsaya takara a shekarar 2023 da kuma tattaunawa da su.

Har ma yayi iƙirarin cewa, zai karbi mulkin Najeriya daga hannun shugaba Buhari a shekarar 2023 don ci gaba da kyawawan ayyuka da kuma ciyar da jam’iyyar APC gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!