Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Na yi farin ciki ƙwarai da sakin ɗaliban Jangeɓe – Buhari

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi matukar farin ciki da samun labarin sakin ‘yan matan sakandiren Jangebe da ke jihar Zamfara.

Da asubahin yau talata ne da misalin karfe hudu daidai aka samu labarin sakin ‘yan matan na makarantar sakandiren Jangebe su 270.

Sai dai tun farko wasu bayanai sun ce daliban da aka sace sun kai 317

A cikin wata sanarwar mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, shugaba Buhari ya ce, ci gaba da bai wa ‘yan bindiga kudin fans aba abin da zai haifar sai kara karfafa musu gwiwa wajen aikata ta’addancin da suke yi.

‘‘Na yi matukar farin ciki, kuma ina ta ya ‘yan uwa da iyalan daliban murna, kuma ina tabbatar musu cewa gwamnatin mu za ta ci gaba da aiki tukuru wajen ganin an kawo karshen matsalar’’. Inji shugaba Buhari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!