Labarai
Nada Mahmud Yakubu a matsayin Ambasada abun kunya ne- ADC

Jam’iyyar adawa ta ADC, ta bukaci tsohon shugaban hukumar zaɓe ta Najeriya INEC Farfesa Mahmood Yakubu, da ya ƙi karɓar muƙamin jakada da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya sanya sunansa cikin wadanda zai nada a matsayin sababbin jakadu.
ADC, ta kuma siffanta naɗin Farfesa Yakubu, wanda ya bar muƙamin hukumar shugabancin INEC a watan Oktoba da ya gabata, inda ta bayyana yunkurin nadin nasa a matsayin abun kunya.
Haka kuma ADC na kallon naɗin Mahmud Yakubu a matsayin abun kunya da rashin sanin ya kamata musamman cikin shekaru biyu da jagorantar zaɓe mai cike da cecekuce da ya bai wa Shugaban Ƙasa Tinubu nasara, a cerwar ADC cikin wata sanarwa.
A ranar Asabar ne fadar shugaban ƙasar ta sanar cewa Tinubu ya nemi ammincewar majalisar dattawan ƙasar domin tura jakadu 32 ƙasashen waje, ciki har da Farfesa Yakubu.
You must be logged in to post a comment Login